Isa ga babban shafi
CPJ

CPJ ta karrama Ahmed Abba na RFI hausa

Kungiyar  kare hakkin ‘yan jaridu ta duniya CPJ ta bayyana sunayen ‘yan jaridun da suka lashe kyautarta ta bana saboda rawar da suka taka wajen aikin jarida, in da ta bayyana  Ahmed Abba, wakilin sashen hausa na Radio France International daga Kamaru da Patricia Mayoga daga kasar Mexico da Pravit Rojanaphruk daga kasar Thailand da kuma Afrah Naseer daga kasar Yemen a matsayin wadanda suka lashe kyautar ta shekarar 2017.

Ahmed Abba, Wakilin sashen hausa na Radio France International
Ahmed Abba, Wakilin sashen hausa na Radio France International © RFI-KISWAHILI
Talla

Cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta CPJ mai ofishi a birnin New York na Amurka ta ce, wadannan ‘ya jaridu da suka lashe kyautar sun fuskanci wulakanci daga bangaren gwamnati da barazanar kisa da kuma dauri a yayin wallafa labarai na gaskiya.

Wakilin sashen hausa na Radio France International Ahmed Abba da gwamnatin Kamaru ta kama a shekarar 2015 bisa zargin alakarsa da kungiyar Boko Haram, an yanke ma sa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari duk da cewa, ya musanta zargin kuma sunansa ne na farko ta CPJ ta gabatar.

Ita kuwa Patricia Mayorga, wakiliyar mujallar Proceso a Mexico, ta shiga wannan sahun ne bayan barazanar kisa da aka yi ma ta sakamaon rahotonta kan alakar Jam’iyyar kasar mai mulki da kuma miyagun ayyuka da suka hada da satan jama’a har ma da cin zarafin fararen hula.

Shi kuwa Pravit Rojanaphruk na Thailand ya samu wannan karramawar ce bayan gwamnatin kasar ta ci mutuncinsa tare daure shi har sau biyu saboda rahotanninsa kan siyasa da kuma kare hakkin bil-adama.

Sai kuma Afrah Naseer, fitacciyar ‘yar jarida a Yemen, wadda aka tirsasa ma ta neman mafaka a Sweden bayan an yi barazanar daukan ranta saboda rahotanninta kan keta hakkin dan adam da cin zarafin mata da kuma dakile ‘yancin ‘yan jaridu da gwamnatin kasar ke yi.

Daraktan kungiyar Joel Smith ya ce ana bada irin wannan kyauta ne ga ‘yan jaridun da suka fuskanci barazanar kisa ko dauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.