Isa ga babban shafi
Rasha-Saudiya

Saudiya ta koma yin hulda da Rasha

Sarkin Salman na Saudiya da shugaban Rasha Vladimir Putin sun sanya hannu kan yarjejeniyar biliyoyin daloli da ta kunshi cinikin makamai da makamashi a ziyarar farko da wani Sarkin Saudiya ya kai a Rasha.

Shugaban Rasha Vladimir Putin na ganawa da Sarki Salman na Saudiya a Moscow
Shugaban Rasha Vladimir Putin na ganawa da Sarki Salman na Saudiya a Moscow Sputnik/Alexei Nikolsky/Kremlin via REUTERS
Talla

Saudiya da ke amintaka da Amurka tana son karfafa huldarta da Rasha, inda ta kulla cinikin sayen makamai da jiragen yaki daga kasar.

Shugabannin na Saudiya da Rasha sun kuma tattauna kan tsawaita yarejeniyar OPEC ta rage fitar da danyen mai a kasuwa.

Wannan ce ziyarar farko da wani Sarki a Saudiya ya taba kai wa a Rasha.

Shugaban Rasha ya ce yana fatar ziyarar za ta kasance tubalin karfafa hulda tsakanin kasarsa da Saudiya.

A tarihi, Saudiya ce kasar da ta fi sayen makaman Amurka, amma yanzu ga alamu tana son bunkusa hulda da Rasha watakila saboda matsayinta a arzikin mai da rawar da ta ke takawa a rikicin Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.