Isa ga babban shafi

Rikici zai fi muni a kasashen Syria da Yemen cikin shekarar 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta kadamar da gidauniyar neman agaji daga manyan kungiyoyi, da kasashe duniya, domin tara dala biliyan 22 da miliyan 500, domin kula da mutane miliyan 90 a shekara mai kamawa ta 2018.

Hoton kundin rahoton hasashen da majalisar Dinkin Duniya ta yi, kan kasashen da zasu fuskantar kalubalen yaki a shekarar 2018, wanda aka wallafa fi a birnin Geneva, da ke Switzerland. Ranar 1 ga Disamba, 2017.
Hoton kundin rahoton hasashen da majalisar Dinkin Duniya ta yi, kan kasashen da zasu fuskantar kalubalen yaki a shekarar 2018, wanda aka wallafa fi a birnin Geneva, da ke Switzerland. Ranar 1 ga Disamba, 2017. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Majalisar ta ce bukatar taimakon zaifi karkata ne musamman don agazawa miliyoyin mutanen da yaki ya shafa ko kuma zai shafa a nahiyoyin Africa da yankin Gabas ta Tsakiya.

Kasashen da majalisar ta ce zasu fi bukatar agajin na dala biliyan ashirin da biyun, sun hada da, jamhuriyar Afrika ta tsakiya, Jamhuriyar Congo, Libya, Somalia, Sudan ta Kudu, Burundi, Kamaru, Sudan, Najeriya, sai kuma Yemen da Syria.

Rahoton ya yi hasashen cewa kasashen Syria da Yemen, sune zasu fi kowane bangare fama da rikici da kuma munin yanayi na wahala ko kuncin rayuwa da al'ummar kasashen zasu fada, sakamakon kazantar yake-yake.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.