Lula Da Silva ya mika kan sa zuwa yan sanda a Brazil
Bayan share kwanaki uku a cibiyar kungiyar kwadagon ma’aikatan karafe na Sao Bernado, tsohon Shugaban kasar Brazil Lula Da Silva ya mika kan sa zuwa jami’an tsaron Curtiba dake kudancin kasar inda suka tisa keyar sa zuwa gidan kaso da zai share shekaru 12 a tsare bisa laifi rashawa da cin hanci.
Wallafawa ranar:
Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa magoya bayan Lula da suka yi kokarin hana yan sanda ficewa da Lula Da silva daga Sao Bernado.
Lula Da Silva mai shekaru 72 na daga cikin yan siyasa da ake sa ran zai tsayawa takara a zaben kasar.
Alkali Moro da ya yankewa Lula hukunci ya bukaci a ba shi kulawa da ta dace a matsayin sa na tsohon Shugaban kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu