Isa ga babban shafi
Brazil

Tsohon Shugaban Brazil Lula zai kai kansa inda ake nemansa

Tsohon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio da Silva ya fadawa taron magoya bayansa yau cewa zai kai kansa inda wata kotun kasar ta nemeshi ya je don fara wa'adin zaman kaso na shekaru 12 saboda zargin rashawa.

Tsohon shugaban Brazil Lula da Silva cikin wani hotro a shekara ta 2016.
Tsohon shugaban Brazil Lula da Silva cikin wani hotro a shekara ta 2016. rfi
Talla

A garin sa na haihuwa Sao Bernardo do Campo yayi wannan alkawari gaban dafifin jama'a da suka fito tarbansa bayan da ya fito daga inda yake samun  mafaka a wani gini bayan da kotun kasar ta nemi ya kai kansa don fara zaman kaso saboda zargin cin hanci tun ranar Alhamis

Ya bayyana cewa alkalin kotun dake yaki da cin hanci da rashawa a kasar Sergio Moro yayi masa kazafi ne kawai cewa ya karbin wani gini na gida daga wani kamfani a lokacin da yake bisa madafun iko, a matsayin cin hanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.