rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Iran Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran

media
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana janye kasar daga cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran saboda abin da ya kira kura-kuran da ke ciki, yayin da ya bayyana kakaba wa kasar sabbin takunkumin karayar tattalin arziki.


Yayin bayyana dalilin daukar matakin, shugaba Trump ya ce, tun farko ba a kulla yarjejeniyar ta hanya mai kyau ba, ganin yadda Iran ke ci gaba da yi wa duniya barazana da kuma goyan bayabn ayyukan ta’addanci.

"Ina sanar da ku yau cewar Amurka za ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, saboda yarjejeniyar ba ta yi komai ba wajen hana Iran ayyukanta na ruguza kasashe da kuma goyan bayan ayyukan ta’addanci" in ji Trump

Shugaban ya kara da cewa "za mu kaddamar da shirin takunkumin tattalin arziki mafi girma akan Iran. Duk wata kasa da ta taimaka wa Iran wajen shirin samun makamin nukiliyarta, za ta fuskanci takunkumi mai karfi daga Amurka. Amurka ba zata amince ayi garkuwa da ita ba."

"Kasar Amurka ta daina barazanar karya, idan na yi alkawari ina cikawa. Fitarmu daga cikin yarjeniyar za ta bamu damar aiki da kawayenmu domin samun yarjejeniya ta gaskiya mai dorewa wadda za ta kawo karshen barazanar Iran" a cewar Donald Trump.

Gabanin wannan mataki na Trump, manyan kasashen duniya da Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci shugaban da ya mutunta yarjejeniyar, musamman ma ganin yadda Iran ke cika sharuddan da aka gindaya mata.