Isa ga babban shafi
Amurka

Ina dakon Kim game da tattaunawarmu-Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, yana dakon wasika daga takwaransa na Korea ta Arewa game da yiwuwar tattaunawa tsakaninsu kamar yadda suka tsaida 12 ga watan gobe a Singapore, yayin da a bangare guda Sakataren Waje na Amurka Mike Pompeo ke ganawa da jami'an Korea ta Arewa don tsaida shawara daya game da wannan ganawa.

Kim Jong-Un da  Donald Trump
Kim Jong-Un da Donald Trump SAUL LOEB / AFP / KCNA VIA KNS
Talla

A dai dai wannan lokaci ne kuma Ministan Waje na Rasha Sergei Lavrov ke kan hanyar ganawa da manyan jami'an gwamnatin shugaban Korea ta Arewa  a Pyongyang .

Wani na hannun daman shugaban Korean, Kim Yong Chol ya kasance babban jami'in Korea ta Arewa na farko da ya ziyarci Amurka cikin shekaru 18 kuma ya gana da Sakataren Waje na Amurka Mike Pompeo, in da har suka ci abincin dare tare.

Karo na uku kenan da manyan jami'an kasashen biyu ke taro don ganin babban taron mai tarihi tsakanin shugabannin kasashen biyu ya yiwu ranar 12 ga watan gobe.

Ita dai Amurka na son ganin Korea ta Arewa ta daina dukkan ayyukan samar da nukiliya da ta ke yi ne don samun sassaucin takunkumin da aka malkaya ma ta.

Wasu masana harkokin siyasar duniya na ganin Korea ta Arewa ba za ta amince ba, sai idan har an ba ta tabbacin cewa Amurka ba za ta yi wani abin da zai kai da hambarar da gwamnatinta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.