Isa ga babban shafi
MDD

Kasashen duniya sun yi asarar Dala tiriliyan 2

Majalisar Dinkin Duniya ta ce manyan masifu masu alaka da sauyin yanayi, sun jawo tafka hasarar Dala tiriliyan 2 da biliyan 25 a kasashen duniya cikin shekaru akalla 20 da suka gabata zuwa yanzu.

Yadda ambaliyar ruwan Tsunami ta yi barna a Japan
Yadda ambaliyar ruwan Tsunami ta yi barna a Japan Reuters/Aly Song
Talla

Rahoton da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar a wannan Laraba ya nuna cewa an samu hau-hawar yawan asarar da irin wadannan masifu na girgizar kasa da ambaliyar ruwa da kuma mahaukaciyar guguwa ke haifarwa a kasashen duniya da akalla kashi 250 kan 100 cikin shekaru 20.

Kazalika wani rahoto da masana suka fitar a baya-bayan nan kan wannan al’amari ya nuna cewa, a tsakanin shekarun 1978 zuwa 1997 an tafka asarar Dala biliyan 895 a dalilin irin masifun da suka afka wa kasashen duniya.

Sai dai a shekarun 1998 zuwa 2017, binciken masanan, ya nuna cewa masifun masu alaka da sauyin yanayin sun haddasa tafka asarar Dala triliyan 2 da biliyan 25.

Kididdiga ta nuna cewa, kasashen da suka fi jin jiki, wajen tafka asarar sun hada da Amurka da China da Japan da kuma India.

Kididdigar ta kuma ce, an samu aukuwar masifun ambaliya da gobarar daji da girgizar kasa da guguwa, har sau dubu 6 da 600 daga 1998 zuwa 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.