Isa ga babban shafi
Venezuela-Amurka

Sabbin takunkuman Amurka za su fara aiki kan Venezuela

Yau lahadi ne sabbin takunkuman Amurka kan man fetur din Venezuela za su fara aiki, dai dai lokaci da rikici ke ci gaba da tsananta hade da matsain rayuwa da kuma yunwa.

Jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa
Jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa ©REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Da misalin karfe 12 na ranar yau ne wa’adin haramcin sayen man fetur din Venezuela zai fara, yayinda ta fitar da wata sanarwa da ke nuna cewa za ta dauki mataki kan duk wata kasa da ta yi tagaciya wajen ci gaba da cinikayya da Venezueler.

Kazalika cikin sanarwar da gwamnatin Amurka ta fitar a yau, ta ce sabbin takunkuman za kuma su shafi wasu asusun ajiyar jiga-jigan gwamnatin Maduro.

Kawo yanzu dai shugaba Nicolas Maduro ya ki amincewa da sauka daga mulki, kamar yadda Amurka ke fata, dai dai lokacin da matsin rayuwa talauci da kuma rsashin aikin yi ke tilastawa al'ummar kasar gudun hijira zuwa wasu kasashen duniya galibi nahiyar Turai.

Yanzu haka dai kasashen duniya 50 galibi na yankin Latin Amurka da kuma kungiyar Tarayyar Turai sun nuna goyon baya ga Juan Guaido tsohon dan majalisa da ya nada kansa matsayin shugaban rikon kwarya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.