Isa ga babban shafi
Najeriya

Jihar Sokoto ce mafi tsananin talauci a Najeriya-Rahoto

A bayanan baya-bayan nan da Ofishin kididdiga na kasa a Tarayyar Najeriya ya fitar, ya nuna cewar har ya zuwa karshen shekarar 2012,  Jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso yammacin Najeriya ita ce mafi tsananin talauci a kasar.

Gwamman Sokoto Alh Aliyu Magatakarda Wamakko
Gwamman Sokoto Alh Aliyu Magatakarda Wamakko thenation
Talla

Bayanan sun nuna cewar a cikin jihohin da ke da yawan Talauci daya haura kashi 70, akwai jihar Katsina mai kashi 74.5% sai Adamawa mai kashi 74.2% sai Gombe mai kashi 74.6% sai Jigawa mai kashi 74.1 sai Filato mai kashi 74.1% sai Ebonyi mai kashi 73.6% sai Bauchi mai kashi 73% sai Kebbi mai kashi 72% sannan Zamfara mai kashi 70.8%.

Jihar Neja na da kashi 33.8% kuma ita ce mafi karancin talauci a Najeriya, sannan Osun mai kashi 37.9% da kuma Ondo mai kashi 45.7.

Sauran Jihohin masu talauci kasa da kashi 50% sun hada da Bayelsa mai kashi 47% da kuma Legas mai kashi 48.6%.

Haka ma a kididdigar da aka gudanar har yanzu yankin Arewacin Najeriya na kan gaba a bangaren tsananin talauci, kuma ya fi kamari a yankin Arewa maso yammacin kasar.

Yankin na Arewa maso yamma dai shi ne ke da kashi 71.4% na yawan talaucin da ake fama da shi a Najeriya, sannan Arewa maso gabashin kasar mai kashi 69.1% sannan Arewa ta tsakiya mai kashi 60.7.

Yankin kudu maso yammaci ne mafi karancin talauci da kashi 49.8% sannan yankin kudu maso kudanci mai kashi 55.5% sannan yankin kudu maso gabashi mai kashi 59.5.

Amma da ya ke karba tambayar manema labarai, Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto Barista Mukhtari Shehu Shgari, ya musanta cewar jihar Sokoto ce mafi kamarin talauci a Najeriya.

Barista Shagari ya bayyana cewar a nasu zato akwai Siyasa a cikin wannan rahoton da hukumar kididdiga ta tarayyar Najeriya ta fitar, yana mai cewa al’ummar Jihar Sokoto wadatattu ne ta ko wane fanni.

Yace al’ummar Jihar manoma ne, kuma idan aka lura da yadda ko a halin yanzu Buhun Albasa ke da tsada, Amma Sakkwatawa ne ke nomanta, hakan zai sa ba za’a alakanta Jihar Sokoto da talauci ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.