Isa ga babban shafi
Masar

An yi zanga zangar goyon bayan Morsi a Masar da Afghanistan

An gudanar da zanga-zanga da musayar wuta tsakanin masu goyon bayan hambararren shugaban kasar Masar Muhammad Morsi da Sojin gwamnati. Sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin sojin gwamnatin kasar Masar, da magoya bayan Muhammad Morsi da soji suka cire daga daga Karagar mulkin kasar , bayanai na nuna cewar akalla mutane 3 ne suka rasa rayukan su.Manema labarai sun bayyana cewar an kuma samu wasu jerin zanga-zangogi a sassa daban daban na fadin kasar ta Masar tare da nuna rashin amincewa da cire Morsi daga Mulkin kasar.Ko a kasar Afghanistan ma an bada labarin barkewar zanga-zanga bayan tashin daga Masallacin Jumu’a.Masu zanga-zangar dai na cewar “Soji kun ji kunya, Morsi muna tare da kai”Masu zanga zangar dai sun tashi ne daga babban Masallacin Kabul ne zuwa wani wurin daban.Daya daga cikin masu zanga-zangar Mohammad Nabi Ahmadzai na cewar ba zai ji tsoron mutuwa ba, saboda jam’iyyar ‘yan uwa musulmi, kuma ina goyon bayan Morsi.A dayan gefen kuma jami’an tsaro na sa ido kan yadda zanga-zangar ke gudana, kuma an kammala zanga-zangar ne, ba tareda jimma kowa rauni ba. 

Wasu magoya bayan hambararren shugaba Mohamed Morsi
Wasu magoya bayan hambararren shugaba Mohamed Morsi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.