Isa ga babban shafi
Burundi

An gano wasu manyan Kaburbura a Burundi

Hukumar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International tace ta gano wasu manyan kaburbura guda biyar a kusa da Bujumbura inda jami’an tsaron Burundi suka binne gawarwakin mutanen da suka kashe.

Amnesty ta nuna hoton Kaburburan da aka binnen gawarwakin mutane a Burundi
Amnesty ta nuna hoton Kaburburan da aka binnen gawarwakin mutane a Burundi Amnesty
Talla

Wannan kuma na zuwa ne a yayin da rahotanni suka ce mahukuntan Burundi sun kame wasu ‘Yan jarida na kasashen waje.

Burundi ta cafke ‘Yan jaridar ne guda biyu Jean-Philippe Remy da ke aiko wa Jairdar Le Monde ta Faransa da labarai daga kasar da kuma wani dan jaridar maid aurar hoto na Birtaniya Phil Moore.

Amnesty ta nuna wasu hotuna a tauraron dan adam da ke nuna kaburburan da aka binne gawarwakin mutane kusa da birnin Bujumbura fadar gwamnatin Burundi.

Mutane kusan 90 aka kashe a samamen da jami’an gwamnati suka kaddamar akan ‘Yan adawa a kasar.

Burundi dai ta fada cikin rikici tun a watan Afrilun 2015 lokacin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya ayyana matakin neman wa’adin shugabanci na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.