Isa ga babban shafi
Habasha

An bukaci sakin 'Yan Jaridu da aka garkame a Habasha

Kungiyar dake kare hakkin ‘yan Jaridu ta duniya, ta bukaci hukumomin kasar Habasha da su gaggauta sakin yan jaridun da suka garkame a kasar.

Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn yayin jawabi ga taron 'yan jaridu a babban birnin kasar Addis Ababa.
Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn yayin jawabi ga taron 'yan jaridu a babban birnin kasar Addis Ababa. Photo: Reuters/Tiksa Negeri
Talla

Jami’ar dake kula da nahiyar Afirka, Angela Quintal tace, yanzu haka yan jaridu 4 ke tsare a hannun hukumomin Habasha cikin su harda Editan wata Jarida Befkadu Hailu.

Wani dan Jarida dan kasar Habasha da ke gudun hijira a kasar Kenya da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, tsare Befkadu na da nasaba da sukar gwamnatin kasar kan rawar da ta taka game da rikicin yankin Oromia da ke kasar.

Kungiyoyin kare hakkin Dan’adam sun dade suna sukar yadda hukumomin Habasha ke kama mutane tana tsarewa ba tare da shari’a ba, kuma yanzu haka akalla mutane 11,000 ake zargin suna tsare a kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.