Isa ga babban shafi
Nijar

Masu zanga zanga sun yi arangama da ‘yan sanda a Torodi dake Nijar

A garin Torodi da ke kusa da iyakar Nijar da Burkina Faso, a jiya litinin jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa-kwalla domin tarwatsa gungun masu zanga-zangar neman a sako shugaban wata kungiyar fararar hula, wanda aka kama saboda ya nuna adawa da yunkurin sayar da wasu jakuna da hukumomi suka kwace daga hannun ‘yan kasuwa a daidai lokacin da ake kokarin tsallakawa da su zuwa Burkina Faso.

kasuwar jakuna  aJamhuriyar Nijar
kasuwar jakuna aJamhuriyar Nijar
Talla

Nijar dai ta kafa dokar hana fita da jakuna zuwa waje, lura da yadda wannan dabba ke neman karewa, to sai dai kungiyoyin fararen hular ba wai suna adawa da aiwatar da dokar ba ne, sai dai yadda jami’an tsaro ke kokarin sayar da jakunan bayan sun kwace su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.