Isa ga babban shafi
Mali

Ana zanga-zangar adawa da zaben raba gardamar a Mali

Dubban ‘yan kasar Mali sun fantsama a kan titunan domin nuna adawarsu da yunkurin gwamnati na shirya gudanar da kuri’ar jin ra’ayin a kan bukatar sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Al'ummar Mali na zanga-zanga kan sauya kudin tsarin mulki
Al'ummar Mali na zanga-zanga kan sauya kudin tsarin mulki REUTERS/Idrissa Sangare
Talla

Daga cikin kwaskwarimar da gwamnatin ke san a yi wa kundin tsarin mulkin kasar dai akwai batun, karawa shugaban kasar Boubacar Keita karfin iko, kirkirar sabbin yankuna a kasar ta Mali, sai kuma amincewa da kafuwar yankin kabilar Tuareg.

Kungiyoyin fararen hulan kasar, da ma ‘yan adawa, sun yi watsi da yunkurin, kasancewar karawa Boubacar Keita karfin iko, yana nufin zai iya zabar rabin wadanda zasu zama ‘yan majalisar dattawan kasar.

Haka zalika yana da ikon sauya Fira ministan kasar a duk lokacin da yaso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.