Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC za ta koma kotu kan kiranyen Melaye

Hukumar Zaben Najeriya ta ce za ta koma kotu domin neman mafita dangane da yadda Sanata Dino Melaye ya ki karbar takardun bukatar kiranye da ta ke neman mika masa.

Senator Dino Melaye da ke wakiltar Kogi ta yamma a Najeriya
Senator Dino Melaye da ke wakiltar Kogi ta yamma a Najeriya Dino facebook
Talla

Rahotanni sun ce Sanata Dino Melaye na ta wasan buya da jami’an hukumar zaben domin kaucewa karbar takardun, kuma kokarin ba shi takardun ofishinsa da hukumar ta yi a jiya bai yi nasara ba, lokacin da jami’an suka ziyarci ofishin sa a zauren Majalisar.

Bayanai sun ce Sanatan Melaye ko dai ya gudu daga Majalisar ko kuma ya garkame kansa a cikin ofis domin kaucewa karbar takardun.

Daraktan yada labarai Oluwole Ozzi ya ce za su koma kotu domin neman mafita kan lamarin.

Amma Sentana Melaye ya ce ya ki amincewa da takardun kiranyen daga INEC domin karan tsaye ne ga kundin tsarin mulki na 1999.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.