Isa ga babban shafi
Mali

Wasu Mahara sama da 30 a Mali sun kona motoci dakayayyakin aikin gina Madatsar Ruwa a Djinee

Yan bindiga sun kai hari tare da lalata wani bangare na madatsar ruwa da ake kan ginawa a yankin Djenne da ke Mopti a tsakiyar kasar Mali.

kasuwar  Djenné, a gaban masalacin garin.
kasuwar Djenné, a gaban masalacin garin. Wikimedia commons/CC BY 3.0/Devriese
Talla

Aikin da ake sa ran a kammala cikin watanni 4 masu zuwa yanzu ya tabbata sai an sake an sake jiran wasu watanni nan gaba, aikin da aka kiyasta cewa zai lakume kudin CFA biliyan 35 na tafiya ne ta fannoni guda uku da zasu kara inganta rayuwar mutan.

A Wani bangare aikin ya tanadi gina gadar mota akan madatsar domin hada mutan Djenee da wasu garuruwa da kogin ya raba.

Kawo yanzu dai da ake cikin wannan aikin Mutan Djene na amfani da kananan kwale kwale ne wajen tsallaka kogin Bani, dake da muhimmanci a makale ga babban kogin Niger.

Idan dai har aka kammala wanan katafaren aiki rayuwar mutan Djine da na sauran wannan yanki na kasar Mali zata canza, inda aka kiyasta cewa, ruwan da madatsar zata tara zai samad da dausayi ga kimanin Kasar noma mai fadin maraba’in Eka dubu 50 .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.