Ana guje wa abincin kan hanya saboda kwalera a Nijar
A jamhuriyar Nijar, alkaluma na baya-bayan nan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na nuni da cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar amai da gudawa wato Kwalara sun kai 67 a halin yanzu, kuma mafi yawansu a jihar Maradi. A jimilce mutane dubu 2 da 752 ne suka kamu da cutar a sassan kasar, in da a Maradi kawai aka samu asarar rayukan mutane 55. Tuni mutane suka yi ban kwana da cin abincin kan hanya saboda wannan annubar kamar yadda za ku ji a rahoton wakilinmu daga Maradi, Salissou Issa.
Wallafawa ranar:
Ana guje wa abincin kan hanya saboda kwalera a Nijar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu