Isa ga babban shafi
Afrika

Nijar ta yi bikin cika shekaru 61 da zama Jamhuriya

Yau 18 ga watan Disemba Jamhuriyar Nijar ke bikin cika shekaru 61 da zama Jamhuriya, dama ce ga shugaban kasa na gabatar da  jawabi ga al’ummar kasar kan halin da ake ciki.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou RFI
Talla

A jawabi da Shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya gabatar zuwa yan kasar ,ya na mai bayyana sabin matakan da gwamnatin kasar tadau domin  tabbatar da tsaro da kuma sake karfafa hulda da wasu kasashe dangane da yaki da yan ta'adda masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.

Shugaba Issoufou ya bayyana tsarin samar da cimaka mai rahusa , tsarin da gwamnatin Nijar za ta  mayar da hankali  ganin karancin abinci ko cimaka da ake fuskanta  a wasu sassan kasar.

A karshe Shugaban kasar ya jaddada aniyar sa ta sauka daga karagar mulki tareda shirya zabe cikin lokaci da kuma mika mulki zuwa zabbaben Shugaban kasa .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.