Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu na karshe a zamanin mulkin farar fata ya rasu

Tsohon shugaban Kasar Afirka ta kudu, farar fata na karshe da ya jagoranci kasar, Frederik de Klerk ya rasu yau alhamis yana da shekaru 85 a duniya.

FW de Klerk, shugaban farar fata na karshe a Afirka ta Kudu.
FW de Klerk, shugaban farar fata na karshe a Afirka ta Kudu. AFP PHOTO / JOHN MACDOUGALL
Talla

De Klerk da shugaban Afirka ta Kudu bakar fata na farko Nelson Mandela sun karbi kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekarar 1983 saboda rawar da suka taka wajen kawo karshen nuna wariyar jinsi a kasar.

A ranar 2 ga watan Fabarairun shekarar 1990, tsohon shugaba Frederick de Klerk ya dage haramcin da aka yiwa Jam’iyyar ANC ta Nelson Mandela da wasu kungiyoyin faftukar karbar ‘yanci a Majalisar dokokin Afrika ta Kudu tare da sakin Mandela da aka tsare na shekaru 27 a gidan yari, matakin da ya baiwa bakaken fata damar shiga siyasar kasar da kuma samun shugaban kasa bakar fata na farko, wato Mandela.

De Klerk ya bayyana cewar yana fama da cutar kansa ko kuma sankara a ranar 18 ga watan Maris na wannan shekara, lokacin da ya cika shekaru 85 a duniya, yayin da Gidauniyar sa ta sanar da cewar cutar sankarar ce tayi sanadiyar mutuwar ayau bayan ya dade yana fama ad ita.

Sanarwar tace tsohon shugaban ya rasu ya bar iyalin sa Elita da ‘yayan sa Jan da kuma Susan, tare da jikoki, kuma nan gaba kadan iyalan zasu sanar da yadda jana’izar sa zata gudana.

An haifi Frederick de Klerk a Johannesburg daga cikin mutanen da ake kira Afrikaners, wato fararen fatar da suka fito daga Netherlands suka kuma yiwa kasar mulkin mallaka, yayin da mahaifin sa ya zama dan majalisar dattawa a gwamnatin masu nuna wariyar jinsi, kuma ya rike mukamin shugaban kasa na wucin gadi na dan gajeren lokaci.

Tsohon shugaban yayi karatun aikin lauya a jami’a, kafin ya lashe kujerar dan majalisa a karkashin jam’iyyar da ta aiwatar da manufofin wariyar jinsi.

De Klerk ya rike mukaman ministoci da dama, kafin ya zama shugaban kasa a shekarar 1989, mukamin da ya rike har zuwa lokacin da ya mika mulki ga zababben shugaba kasa Nelson Mandela a zaben dimokiradiyar kasar na farko a shekarar 1994.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.