Isa ga babban shafi
gambia - siyasa

Barrow ya kama hanyar tazarce a shugabancin Gambia

Shugaban Gambia mai ci Adama Barrow na kan gaba a samakon farko na wasu yankuna da aka fitar bayan zaben ranar Asabar dake matsayin zakaran gwajin dafi ga demokradiyar kasar bayan Yaya Jameh.

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow,05/12/21.
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow,05/12/21. AFP/File
Talla

Barrow wanda ya kawo karshen mulkin Yahya Jammeh na shekaru 22, yanzu haka ya kama hanyar tazarce a wa’adi na biyu, bayan da sakamakon farko na hukumar zaben kasar ya nuna shi ke kan gaban babban abokin hamayyarsa Ousainou Darboe  a kusan gundumomi 40, daga cikin 53 na fadin kasar.

Wani jami'in hukumar zaben ya shaidawa manema labarai a Banjul babban birnin kasar cewa ya kamata a bayyana sakamakon karshe da yammacin wannan Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.