Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Murar tsuntsaye: An tafka hasarar kaji kusan dubu 500 a Burkina Faso

Akalla kajin da yawansu ya kai rabin miliyan ne suka mutu sakamakon barkewar cutar murar tsuntsaye ta H1N1 a Burkina Faso.

Murar tsuntsaye ta janyowa masu kiwon kaji tafka hasara a Burkina Faso.
Murar tsuntsaye ta janyowa masu kiwon kaji tafka hasara a Burkina Faso. © REUTERS/Luc Gnago
Talla

Bayanai sun ce kajin sun mutu ne ta dalilin murar tsuntsayen kai tsaye, ko kuma ta hanyar kashe su da aka yi, matakin da gwamnati ta dauka domin hana yaduwar cutar.

Ministan albarkatun dabbobi a Burkina Faso Moussa Kabore ya shaidawa taron manema labarai a jiya Asabar cewa an gano bullar cutar ta murar tsuntsaye ce a karshen shekarar da ta gabata a gonaki 42 a wasu yankuna bakwai da ke tsakiya da kuma yammacin kasar.

Ministan ya kara da cewar, ya zuwa ranar 7 ga watan Janairu, baya ga kusan kajin dubu 500,000 da suka mutu sakamakon murar ta H1N1, an kuma lalata kwalayen kwai miliyan 1 da dubu 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.