Isa ga babban shafi
Afirka ta kudu

Wani mutum ya kwace bindigar dan sanda ya kashe majinyata a wani asibiti

Wani mutum a kasar Afirka ta Kudu ya kwace bindiga daga hannun wani dan sanda, inda ya bude wuta kan wani asibiti tare da harbe majiyyata biyu har lahira.

'Yan sandan Afirka ta Kudu yayin tinkarar masu zanga-zanga 14/01/22.
'Yan sandan Afirka ta Kudu yayin tinkarar masu zanga-zanga 14/01/22. AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Sanarwar da kakakin ‘yan sandan Cape Town Birgediya Novela Potelwa ya fitar ta ce, mutumin mai kimanin shekaru 40 ya kuma raunata dan sandan da ya kwace wa makamin.

'Yan sanda sun kai wani mutum ne da ake zargi da aita laifi zuwa asibitin, wanda mutumin ya harbe tare da wani majinyaci, kafin ayi nasarar kwace bindigar da ke hannunsa.

Afirka ta Kudu tana daya daga cikin kasashen duniya da aka fi kashe kashe, wanda ba ta hanyar yaki ba.

A shekarar da ta gabata yawan kashe-kashen da aka yi a Cape Town ya kasance mafi girma a kasar, inda aka kashe 64 a cikin mutane 100,000, idan aka kwatanta da na Johannesburg dake da 37 da na New York ya kai 5.5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.