E-Guinea ta yi barazanar korar jakadan Faransa daga kasar
Mataimakin shugaban Equatorial Guinea, Teodoro Nguema Obiang Mangue, ya yi barazarar korar jakadan Faransa daga kasar a daidai lokacin da alaka ke dada tsami tsakanin kasashen biyu, daga lokacin da aka gurfanar da mataimakin shugaban gaban kotun Paris saboda zargin rashawa.
Wallafawa ranar:
A shekarar da ta gabata ne dai kotun daukaka kara a Faransa ta tabbatar da hukuncin daurin talata na shekaru uku da aka yanke wa mataimakin shugaban kasar ta Guinea bayan samun shi da rashawa da kuma boye makudan kudade a kasar.
Wannan hukunci dai ya share fagen kwace wani katafaren gida mai fadin murabba’in mita dubu da aka kiyarsta cewa zai kai Euro milyan 107 a birnin Paris.
A shafinsa na Twiitter, Obiang ya ce matukar aka fitar da jami’an diflomasiyar Guinea daga cikin wannan gida, to lalle kuwa zai bayar da umurnin tasa keyar jakadan na Faransa a cikin sa’o’I 24.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu