Isa ga babban shafi

Karin mutane 6 sun harbu da Ebola a Uganda bayan mutuwar mutum na farko

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce an samu karin mutane shida da suka kamu da cutar Ebola a kasar Uganda, bayanda kasar ta sanar da sake bullar cutar karon farko tun bayan kawar da ita a shekarar 2019.

Wannan ne karon farko da Ebola ke barkewa a Uganda tun bayan kawar da ita a shekarar 2019.
Wannan ne karon farko da Ebola ke barkewa a Uganda tun bayan kawar da ita a shekarar 2019. AFP/File
Talla

A talatar makon nan ne, ma'aikatar lafiyar Uganda ta sanar da barkewar cutar Ebola a gundumar Mubende da ke tsakiyar kasar inda ta tabbatar da mutuwar wani mutum mai shekaru 24 da cutar ta kashe.

Sanarwa da hukumar WHO ta fitar, ta ce "Ya zuwa yanzu, an tabbatar da cewar mutane bakwai da suka kamu da cutar ta Ebola a Ugandar cikinsu harda mutum gudan da ya mutu.

Tuni dai aka gano mutane 3 da wadanda suka harbu da cutar suka yi mu’amala da su, kari kan mutane 10 da ake tsammanin sun harbu da cutar inda tuni aka fara basu kulawar gaggawa a asibitin Mubenbe.

Daraktan WHO a Uganda, Abdou Salam Gueye ya ce suna aiki kafada-da-kafada tsakaninsu da tawagar jami’an lafiya ta kasar da ke yaki da cutar ta Ebola don daukar matakan baiwa jama’a kariya tare da bayar da cikakkiyar kulawa ga wadanda suka harbu.

Uganda mai iyaka da jamhuriyar demokradiyyar Congo na ganin bullar cutar ta Ebola lokaci zuwa lokaci a shekarun baya-bayan nan, inda ko a 2019 cutar ta kashe mutane 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.