Isa ga babban shafi

Saliyo: An binne mutane 27 da suka mutu tarzomar watan Agusta

An yi jana'izar fararen hula 27 da aka kashe a tarzomar da ta tashi cikin watan Agusta a Saliyo.

Jana'izar binne fararen hula 27 da suka mutu yayin tarzoma kan matsin tattalin arziki a Saliyo
Jana'izar binne fararen hula 27 da suka mutu yayin tarzoma kan matsin tattalin arziki a Saliyo © Saidu BAH AFP
Talla

A ranar litinin aka binne mutanen a Freetown babban birnin kasar, bayan karrama su da gwamnati ta yi, a yayin da iyalansu ke ci gaba da bayyana rashin amincewa da bayanan 'yan sanda suka gabatar kan dalilan mutuwarsu.

A ranar 10 ga watan Agustawata zanga-zangar da aka yi kan tsadar rayuwa ta barke, inda aka yi arrangama tsakanin jami'an tsaro da samari da ke neman shugaba Julius Bio ya yi murabus.

Rikicin da ya barke dai ya fantsama zuwa wasu sassan kasar a waccan lokaci, abinda ya sanya gwamnati kafa dokar hana amfani da intanet domin dakile boren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.