Isa ga babban shafi

Uganda za ta aike da dakaru kusan 1,000 zuwa Congo

Uganda za ta jibge sojoji kusan 1,000 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a karshen watan Nuwamba karkashin rundunar da ke yaki da 'yan tawaye.

Matakin dai na zuwa ne yayin da masu dauke da makamai ke zafafa hare-hare
Matakin dai na zuwa ne yayin da masu dauke da makamai ke zafafa hare-hare AFP - ALEXIS HUGUET
Talla

A 'yan watannin baya-bayan nan dai ana gwabza kazamin fada a yankin da ke da tashe-tashen hankula tsakanin sojojin Congo da 'yan tawayen M23, lamarin da ya sa kungiyar kasashen gabashin Afirka EAC ta tura rundunar hadin gwiwa a yankin domin dakile tashin hankalin.

Sojojin Kenya sun isa kasar ne a ranar 12 ga watan Nuwamba kuma mai magana da yawun rundunar soja da tsaron Uganda Felix Kulayigye ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa tawagar ta Uganda za ta bi su nan bada jimawa ba.

Fadan dai ya sake haifar da tashe-tashen hankula a yankin, inda Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ke zargin makwabciyarta Rwanda da marawa kungiyar M23 baya.

Kigali ta musanta goyon bayan kungiyar M23 tare da zargin Kinshasa da hada kai da tsohuwar kungiyar 'yan tawayen Hutu ta Rwanda da aka kafa a congo, bayan kisan kiyashin da aka yi wa galibin 'yan kabilar Tutsi a kasar Rwanda a shekarar 1994.

M23 na daya daga cikin kungiyoyi kusan 120 da ke dauke da makamai a gabashin Kongo, yawancinsu burbishin yakokin yanki biyu ne da ya barke a karshen karnin da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.