Isa ga babban shafi

Malta ta kama sojojin hayar Birtaniya a kokarin su na shiga Libya

Malta ta sanar da kame wasu tarin sojojin hayar Birtaniya a dai dai lokacin da su ke kokarin tsallakawa birnin Misrata na Libya don taimakawa a yakin shekara-shekaru da ke gudana tsakanin bangarori biyun da ke ikirarin mulkar kasar.

Wasu Sojin haya.
Wasu Sojin haya. AP
Talla

Rahotanni sun ce Sojojin hayar wadanda tsaffin Sojin Birtaniya da suka yi ritaya, na aiki ne da wani kamfanin tsaro mallakin Jack Mann da ke da kusanci da Yarima Harry.

Malta ta sanar da cewa cikin Sojojin hayar da ta kama har da Jack Ma da kansa a lokacin da suke kokarin hawa wani karamin jirgin sama don isar da su Libya.

Malta ta zargi Sojojin da karya dokokin shige da ficen yankin wadanda Majalisar Dinkin Duniya ta gindaya ciki kuwa har da haramtawa Sojojin hayar ratsa cikin kasashen don kai dauki kasar ta Libya mai fama da yakin fiye da shekaru 10.

Wasu majiyoyin labarai sun ruwaito cewa, Sojin hayar sun yi ikirarin kasancewa Sojoji na da Libya ta dauka don horar da dakarunta, sai dai bayan bincike Maltar ta tabbatar da kasancewar Sojojin na haya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.