Isa ga babban shafi

Kazamin fada tsakanin Sojin Somalia da al-Shebab ya kashe daruruwan rayuka

Dakarun Sojin Somalia da Mayakan al Shebab da ke biyayya ga kungiyar al-Qaida sun yi ikirarin kisan mutane fiye da 100 kowannensu yayin wata gwabzawa tsakaninsu a jiya juma’a, gumurzun da ke matsayin mafi muni da bangarorin biyun suka gwabza tun bayan da gwamnatin kasar ta kaddamar da yakin kakkabe barazanar mayaka masu tsattsauran ra’ayi a kasar.

Kakakin kungiyar Al Shebab.
Kakakin kungiyar Al Shebab. © AFP PHOTO/ STRINGER
Talla

Wata sanarwa da gwamnatin Somalia ta fitar ta ce dakarunta sun kashe mayakan al-Shabab fiye da 100 lokacin da suka farmaki wani sansanin Sojin kasar da ke garin Galcad a yankin Galgudud garin da a baya-bayan ya kufce daga ikon mayakan sakamakon matsin kaimin da Sojoji suka yi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa yayin fafatawar anyi asarar Sojoji 7 ciki har da babban Soja guda da ya samu horo na musamman daga Amurka, ko da yake dakarun sun ci gaba da iko da ilahirin yankin ba tare da barin barazanar mayakan ta yi tasiri ba.

Sai dai kakakin mayakan nja Al-Shabab Sheikh Abu Musab ya bayyana cewa yayin fafatawar sun kashe Sojojin Somalia ciki har da manyan ofisoshi fiye da 150.

Babu dai wasu kwararan hujjoji da ke nuna yiwuwar ikirarin kowanne bangare na kan gaskiya sai dai wasu da ke makwabtaka da yankin da gumurzun ya faru sun ce an kwashe tsawon daren jiya juma’a wayewar yau asabar ana musayar wuta tsakanin mayakan da Sojojin.

A bara ne gwamnatin Somalia ta kaddamar da yaki kan mayakan na al-Shabab da nufin kawar da su bayan tsanantar hare-harensu ciki har da munanan hare-hare a Mogadishu babban birnin kasar, lamarin da ya basu damar kwace iko da sassa daban daban a tsakiya da kuma kudancin Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.