Isa ga babban shafi

Rikicin Sudan ya raba yara sama da miliyan daya daga gidajensu - UNICEF

Majalisar Dinkin Duniya tace rikicin Sudan ya raba sama da kananan yara miliyan daya da gidajensu, kuma dubu 270 daga cikinsu a yankin Darfur ne.

Wasu 'yan kasar Sudan da suka tsere daga rikicin Darfur, kusa da matsuguni na wucin gadi a kan iyakar Sudan da Chadi, a ranar 13 ga Mayu, 2023
Wasu 'yan kasar Sudan da suka tsere daga rikicin Darfur, kusa da matsuguni na wucin gadi a kan iyakar Sudan da Chadi, a ranar 13 ga Mayu, 2023 © REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Sanarwar asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ta bayyana cewa ko baya ga yaran da suka rasa matsugunansu, an kashe wasu akalla 330 tare da jikkata kusan dubu 2.

UNICEF yace yanzu haka kimanin kananan yara miliyan 13 ne ke matukar bukatar agajin jin kai a kasar ta Sudan.

Tun a tsakiyar watan Afrilu kazamin fada ya barke a Sudan tsakanin Hafsan Sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar runduna ta Rapid Support Forces (RSF).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.