Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun tilasta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Timbuktu

Kamfanin jirgin sama na 'Sky Mali', wanda shi ne jirgi daya tilo na kasuwanci da ke jigila zuwa Timbuktu, ya dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa birnin saboda rashin tsaro, lamarin da ya sake dagula halin kuncin da mazauna garin da ke arewacin Mali suke ciki, wadanda suka shafe akalla wata guda karkashin kawanyar da ‘yan ta’adda suka yi musu.

Wasu mazauna birnin Timbuktu da ke arewacin kasar Mali.
Wasu mazauna birnin Timbuktu da ke arewacin kasar Mali. © Moulaye Sateh / AP
Talla

Tuni dai birnin na Timbuktu, ya fada cikin kangin fama da karancin abinci da kayayyakin agaji, tun bayan da wata kungiya mai alaka da al Qa'eda ta datse hanyoyin mota da na ruwa da ke shiga cikinsa a tsakiyar watan Agusta.

Da safiyar ranar litinin da ta gabata, rahotanni suka ce an kai hari da makamai a kusa da filin jiragen sama na Timbuktu, lamarin da wasu mazauna yankin biyu suka tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters

Sa’o’i bayan bullar rahoton kai farmakin ne kuma kamfanin jiragen saman na 'Sky Mali' ya sanar da dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragensa zuwa Timbuktu har sai lamarin tsaro ya daidaita.

A makon da ya gabata, kungiyar Tarayyar Turai EU ta ce kawanyar da ‘yan ta’addan suka yi wa Timbuktu ta kara fadada zuwa wasu garuruwa da ke yankin, da suka hada da Rharous, da Niafounké, da Goundam, da Diré, da Tonka, da Ber da kuma Léré.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.