Isa ga babban shafi

Kungiyoyin da ke dauke da makamai a Mali za suyi fito na fito da gwamnatin sojin kasar

Gamayyar kungiyoyin da ke dauke da makamai da suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a Mali, sun ce za su kare kansu daga hare-haren da gwamnatin sojin kasar ke kai musu a yankin Arewacin kasar.

Gamayyar kungiyoyin da ke dauke da makamai a Mali sun ce za suyi fito na fito da gwamnatin sojojin kasar, sabida kare-kansu daga hare-haren da ake kai musu.
Gamayyar kungiyoyin da ke dauke da makamai a Mali sun ce za suyi fito na fito da gwamnatin sojojin kasar, sabida kare-kansu daga hare-haren da ake kai musu. © Soumeylane Ag Anara / AFP
Talla

A cikin sanarwar da kungiyoyin suka fitar, sun bukaci fararen hular da ke zaune a cibiyoyin gwamnati su fice daga cikinsu, lamarin da ke nuna cewar akwai yuwuwar rikici ya barke a tsakanin banagrorin biyu.

Gwamnatin yankin Gao ta sanar da sanya dokar hana fitar dare a yankin na tsawon kwanaki 30, wacce za ta rinka aiki daga 8 na dare zuwa 6 na safe, in banda motocin jami’an tsaro da aka baiwa damar yin zirga-zirga.

Sanarwar da gamayyar kungiyoyin suka fitar, ta biyo bayan harin kunar bakin waken da aka kai wani sansanin soji da ke Arewacin Mali a ranar Juma’a, wanda ke zuwa kwana daya bayan harin da aka kaiwa sojoji da kuma wani jirgin ruwan fasinjojin da ake zargin ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi ne suka kai, da ya hallaka mutane 64.

A baya-bayan nan yankin na fuskantar barazanar hare-hare, tun bayan ficewar sojojin Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.