Isa ga babban shafi

Shugaban Rwanda Kagame ya ce zai yi takarar neman wa’adi na 4

Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara domin neman tazarce a wani wa’adi na hudu.

Paul Kagame, shugaaban Rwanda.
Paul Kagame, shugaaban Rwanda. REUTERS - JEAN BIZIMANA
Talla

A yayin wata ganawa da ya yi ne da jaridar harshen Faransanci ta ‘Jeune Afrique, Paul Kagame, wanda ya jagoranci Rwanda tsawon shekaru da dama ya ce lallai shi dan takara ne a babban zaben kasar mai zuwa.

Jaridar ta ruwaito Kagame, mai shekaru 65 yana bayyana farin ciki da damar da ‘yan kasar Rwanda suka ba shi ya jagorance su, yana mai cewa zai ci gaba da yi musu hidima daidai gwargwadon iko.

A watan Maris ne gwamnatin Rwanda ta yanke shawarar hade ranar zaben majalisar dokoki da ta shugaban kasar, inda ta ce a yanzu za a gudanar da zabukan ne a watan Agustan shekara mai zuwa.

A shekarar 2017 ce Kagame, wanda tsohon dan tawaye ne ya lashe zaben da ta bashi damar yin wa’adi na 3 a matsayin shugaban kasar Rwanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.