Isa ga babban shafi

Ta'addanci ya tilasta kulle kashi 1 bisa 4 na makarantun Burkina Faso

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana takaici kan yadda kananan yara akalla miliyan guda a Burkina Faso suka gaza samun damar fara karatu a sabon zangon karatun shekarar nan sakamakon tsanantar tashe-tashen hankula da karuwar matsalolin tsaro a sassan kasar.

Wata makaranta a Burkina Faso.
Wata makaranta a Burkina Faso. AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

Asusun na UNICEF ya yi gargadin cewa akwai akalla makarantu dubu 6  da 149 ko kuma kiyasin duk makaranta guda cikin 4 da har zuwa yanzu ke ci gaba da kasancewa a kulle cikin kasar ta Burkina Faso sakamakon tsanantar hare-haren ta’addanci.

Alkaluman da UNICEF ya tattara na nuna cewa fiye da dalibai miliyan 1 da malamai dubu 31 basu samu damar komawa makarantu a wannan zangon karatun da aka koma ba, yayinda makarantu akalla 230 yanzu haka ke matsayin matsugununan wucin gadi ga mutane fiye da dubu 52 da matsalolin tsaro ya raba da matsugunansu.

Bayanan da ke kunshe cikin rahoton na UNICEF ya bayyana cewa tabarbarewar matsalolin tsaro ya tilasta kulle tarin makarantu a yankunan da lamarin ya tsananta yayinda tarin dalibai da iyayensu suka gudu daga yankunansu don tsira da rayukansu daga hare-haren ‘yan ta’adda.

Wakilin UNICEF a Burkina Faso John Agbor ya sha alwashin tabbatar da ganin kowanne yaro a kasar ya koma samun karatu yadda ya kamata yana mai cewa  yanzu haka asusun da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi ta kasar sun mayar da yara akalla miliyan 3 da dubu 800 da suka kunshi maza da mata makarantu ciki kuwa har da wadanda suka fito daga yankunan da ta’addanci ya tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.