Isa ga babban shafi

Mun kusa kawo karshen zazzabin cizon sauro a Afirka - UNICEF

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, tare da kungiyar lafiya ta Gavi, sun fitar da sanarwar cewa nan ba da jimawa ba, za a kawo karshen cutar zazzabin cizon sauraro, musamman a wasu kasashen Afirka da cutar tafi kamari, ta hanyar rarraba alluran rigakafin wannan cuta da ke yiwa kananan yara kisan mummuke.

Wani jami'in lafiya da yake bude allurar rigakafin zazzabin cizon sauro a kauyen Ndhiwa da ke Kudancin Kenan, ranar 13 ga Satumba, 2019.
Wani jami'in lafiya da yake bude allurar rigakafin zazzabin cizon sauro a kauyen Ndhiwa da ke Kudancin Kenan, ranar 13 ga Satumba, 2019. AFP - BRIAN ONGORO
Talla

Wannan na zuwa ne, bayan jirgin farko dauke da dubban alluran wannan rigakafi da ya sauka a Jamhuriyar Kamaru, bayan da aka gudanar da gwaje-gwajen rigakafin cutar a kasashen Kenya, Ghana da Malawi, har ma aka samu nasarar rage adadin masu kamuwa da ita fiye da yanda aka tsammata.

Hukumomin lafiyar biyu sun bayyana wannan ci gaba na allura da aka samu a matsayin, musamman wajen kawar da daya daga cikin cutuka mafiya hatsari da ke barazana ga kananan yara a nahiyar Afirka.

Karin asu alluran rigakafin da adadin su ya haura miliyan daya da dubu dari bakwai, nan ba da jimawa ba UNICEF ya ce za a aika su kasashen Burkina Fasio, Laberiya, Niger da kuma Saliyo.

Shugaban UNICEf, Catherine Russell, gabatar da wannan shiri na rigakafi, sjhakka babu zai kawo karshen fargabar da iyaye da kuma hukumomin lafiya ke ciki, game da illar da wannan cuta ke haifarwa a kasashe, musamman masu raunin tattalin arziki.

Kasashen Afirka da dama na shirye-shiryen yadda za su sanya alluran rigakafin zazzabin cizon sauro cikin rukunan rigakafin da ake yiwa yawa, inda ake sa ran za su fara amfani da wannan shiri daga Watan Janairu zuwa Maris din shekarar badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.