Isa ga babban shafi

Dan Afirika ya lashe kyautar gwarzon 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dikin Duniya ta ayyana Abdullahi Mire a matsayin wanda ya lashe kyautar Gwarzon ‘yan gudun hijira ta bana, sakamakon kokarin da yake yi wajen ilimantarwa da kuma samar da litattafan karatu ga dubban ‘yan gudun hijira a kasar Kenya.

Ire-iren litattafan da Abdullahi ke rabawa dalibai
Ire-iren litattafan da Abdullahi ke rabawa dalibai AP - SAURABH DAS
Talla

Matashi Mire mai shekaru 36 ya samar da litattafan karatu ga yara ‘yan gudun hijira sama da dubu 100 a Kenya, musamman wadanda ke sansanin gudun hijira na Dadaab mai cinkoson jama’a.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP Mire ya ce littafi na da matukar tasirin da zai iya sauya rayuwar dan adam.

Burina shine kowanne yaro ya sami cikakken ilimi  ba tare da la’akari da kasancewar sa dan gudun hijira ba, inji Mire.

Da yake sanar da Abdullahi a matsayin wanda ya lashe kyautar shugaban hukumar kula da gudun hijira ta majalisar dinkin duniya Filippo Grandi ya ce Abdullahi wata babbar alama ce da ke nuna cewa rayuwar mutane zata iya inganta ba tare da la’akari da inda suke ba.

Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya Fillippo Grandi
Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya Fillippo Grandi AP - Salvatore Di Nolfi

An dai haifi Mire a kasar Somalia, amma sakamakon rashin zaman lafiya da ya addabi kasar, iyayen sa suka yi gudun hijira zuwa Kenya, lokacin da yake yaro.

Abdullahi ya yi aiki a matsayin dan jarida a kasar Kenya, inda yake bayar da labarin da ya shafi sansanin gudun hijirar a kowacce rana, kuma daga nan ne ya sami dabarar samarwa yara litattafai, bayan da wata karamar yarinya yar shekaru 15 ta roke shi ya taimake ta da littafin Biology.

Kwararre a fannin kimiyyar hallitar dan adam ta Bilogy
Kwararre a fannin kimiyyar hallitar dan adam ta Bilogy © ANNIE RISEMBERG/AFP

Abdullahi ya ce yarinyar wadda ita da iyayen ta ke rayuwa a sansanin gudun hijirar ta gaya masa cewa babban burin ta shine ta zama kwararrriyar likita don ta taimaka wajen rage cututtuka da yawan mace-mace da ake samu a sansanin.

A hankali na fahimci akwai yara da yawa da suke burin da karatu, amma karancin litattafai yana hana su don haka na dauki aniyar neman musu litattafai.

Abdullahi Mire ya kuma bukaci matasa su yi koyi da shi a cewar sa ba wani abu ne mai wahala ba, matukar aka jajirce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.