Isa ga babban shafi

Sojoji a Somalia sun hallaka kafatanin 'yan ta'addar da suka kai hari wani Otal

‘Yan sanda a Somalia sun sanar da mutuwar mutane 9 ciki har da sojoji 3 a sakamakon wata mummunar arangama da sojoji suka yi da mayakan Al-Shabab, wadanda suka kaiwa wani Otal hari a birnin Mogadishu.

Sojojin sun kashe kafatanin mayakan da suka kai harin
Sojojin sun kashe kafatanin mayakan da suka kai harin AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan kasar ta fitar ta ce karin wasu mutane 10 sun jikkata, yayin da aka ceto wasu 84 cikin Otal din da Al-Shabab din ta kaiwa hari.

Bayanai sun ce mayakan sun zagaye Otal din tsahon awowi 13, a wani abu da ba sabo ba, a yanayin yadda kungiyar mai alaka da Al-Qa’ida ta saba kai hari Otal-Otal da sauran guraren taruwar jama’a ta hanyar dasa bam.

Wasu ganau sun shaidawa manema labarai cewa mayakan sun zagaye Otal din Pearl Beach wanda yayi suna wajen tara manyan kusoshin gwamnati.

‘Yan sanda sunce jami’an tsaro sun yi nasarar hallaka kafatanin mayakan da suka kai wannan hari, bayan shafe sama da sa’o’I 15 ana bata kashi a tsakani.

Mazauna zagayen Otal din sun ce ba zasu iya kirga yawan bama-baman da suka tashi a lokacin harin, wanda ya bar mutane da dama cikin jini ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.