Isa ga babban shafi

Tattalin arzikin Sudan ta Kudu na cikin tsaka mai wuya saboda rikici Sudan

Tashe-tashen hankula na iya kara ta'azzara kalubalen da suka dabaibaye Sudan ta Kudu bayan da daya daga cikin manyan bututun manta da ya tashi daga makwabciyarta Sudan zuwa kasuwannin duniya, ya lalace a watan da ya gabata.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir kenan.
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir kenan. AP - Gregorio Borgia
Talla

Lamarin ya faru ne a farkon watan Fabrairu a jihar White Nile ta kasar Sudan, lamarin da ya sa kamfanin mai na Dar ya dakatar da jigilar man.

Fashewar ta faru ne a wani yanki da ke karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa na RSF na Sudan, dake fafatawa da sojojin da ke biyayya ga gwamnatin sojin Sudan don samun madafan iko a kasar.

Tawagar kwararru ta kasar tace an samu tsaikon gyara bututun man ne saboda fadan da ake ci gaba da yi, lamarin da ke kara nuna fargabar cewa tattalin arzikin Sudan ta Kudu zai ruguje.

Bututun ya kunshi kashi biyu bisa uku na kudaden shigar mai da ake samu, abin da ake ganin akwai kalubalen da ke tunkarar kasafin kudin kasar.

Bankin duniya ya bayyana cewa, kashi 90 na kudin shigar da Sudan ta Kudu ta ke samu ya ta’allaka ne kacokan kan man fetur din da take fitarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.