An saki Bafaransar da aka sace a Yemen
Gwamnatin Faransa tace an saki wata yar kasar Isabelle Prime da aka yi garkuwa da ita tun ranar 24 ga watan Fabarairun bana a Yemen, inda ta ke kan hanyar zuwa gida yanzu haka.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da gwamnatin Faransa ta fitar tace Prime na karkashin kulawar jami’anta da ke Yemen, ba tare da Karin bayani akai ba.
Rahotanni sun ce Isabelle Prime ta isa Oman a yau Juma’a bayan sakinta.
An dai kama matar wadda ke aiki da Bankin Duniya tare da mai mata fassara ne a birnin Sanaa, amma daga bisani an saki abokin aikinta a watan Maris.
Babu dai wani bayani akan wadanda suka yi garkuwa da Bafaransar, amma a watan Yuni an nuna ta a wani hoton bidiyo a You Tube.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu