Isa ga babban shafi
Amurka

Kalaman Trump barazana ne ga tsaron Amurka- Pentagon

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana cewa, kalaman dan takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar Republican, Donald Trump barazana ne ga tsaron kasar.

Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican
Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican REUTERS/Mark Kauzlarich
Talla

Trump ya bukaci a haramta wa musulmai shiga Amurka sakamakon harin da wasu ma’aurata musulmai biyu suka kai a wata cibiyar kula da lafiya da ke birnin San Bernardino na jihar California tare da kashe mutane 14, yayin da Pentagon ta ce kiran da ya yi zai iya bunkasa ayyukan kungiyar ISIS mai ikirarin jihadi.

Tuni dai fadar shugaban kasar Amurka ta yi alla-wadai da kalaman na Trump tare da fadin cewa bai cancanci ya karbi ragamar shugabancin kasar ba, kuma ta bukaci jam’iyyar Republican da ta wanke kanta daga kalaman na sa wadanda su ka haifar da cecekuce a sassan duniya.

Amurka dai na jagorantar kasashe wajen kaddamar da haren sama akan kungiyar ISIS a Syria da Iraqi.

A bangare guda, masu rajin kare hakkin dan adam sun bayyana cewa, musulmai a Amurka na fusknatar kyama tun lokacin da kungiyar ISIS ta kaddamar da hari a birnin Paris na kasar Faransa a watan jiya tare da kashe mutane 130.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.