Isa ga babban shafi
Turkiya

Ana zaman makoki a Turkiya bayan harin ta'addanci

Gwamnatin kasar Turkiya ta ayyana zaman makoki a wannan laraba bayan harin ta'addancin da ya hallaka mutane 41 a filin jiragen sama na Ataturk da ke birnin Santanbul na kasar

Kwararru na gudanar da bincike bayan  kaddamar da harin na filin jiragen saman Turkiya da ke birnin Santanbul
Kwararru na gudanar da bincike bayan kaddamar da harin na filin jiragen saman Turkiya da ke birnin Santanbul REUTERS/Murad Sezer
Talla

Gwamnatin kasar na zargin kungiyar IS da kaddamar da harin na jiya wanda aka bayyana a matsayin mafi muni daga cikin kazaman hare hare guda hudu da 'yan ta'adda suka kai wa kasar a cikin wannan shekarar.

Bayanai sun ce, maharan sun bude wuta ne kan mai uwa da wabi a bangaren matafiya  zuwa kasashen duniya kafin daga bisani su tayar da bama-bamai da ke jikinsu.

Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan wanda ya yi Allah wadai da harin ya bukaci hadin kan kasashen duniya domin yaki da ta’addanci.

Ko a watan Octoban bara, sai da gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku sakamakon kazamin harin da aka kai babban birnin Ankara, inda mutane sama da 100 suka mutu kuma an zargi kungiyar IS da kai harin na wancan lokacin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.