Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton ta samu goyon bayan jakadun Amurka

Tsoffin jakadun Amurka 75 cikin su har da 57 da shugabanin Jam’iyyar Republican suka nada, sun bayyana goyan bayansu ga Hillary Clinton ta Democrat,  in da suka ce Donald Trump ba shi da kwarewar da zai rike mukamin shugaban kasa. 

Hillary Clinton da neman shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat
Hillary Clinton da neman shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat REUTERS/William Philpott
Talla

A wata wasika da suka rubuta, tsoffin jakadun sun ce, a matsayinsu na tsoffin jami’an diflomasiya da suka yi aiki da shugabani da dama da suka hada da Harry Truman da Richard Nixon, sun fahimci cewar Trump bai dace ya shugabanci Amurka ba.

Sun bayyana yadda dan takarar ke yaba wa shugaban Rasha Vladimir Putin da kuma sukar hafsoshin sojin Amurka a matsayin babban kuskure.

Jakadun sun ce, Trump bai san kalubalan da Amurka ke fuskanta ba daga Rasha da China da kungiyar ISIS da kuma yaduwar makamin Nukiliya ba, balantana matsalar baki da amfani da miyagun kwayoyi.

Wasikar ta kuma koka kan yadda dan takaran ke sukar kawayen Amurka a duniya, matakin da suke cewa, zai shafi manufofin kasar.

Wannan wasika na zuwa ne kwana guda , bayan wasu Janar Janar na sojin Amurka 15 da suka yi ritaya sun bayyana goyan bayansu ga takarar Hillary Clinton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.