Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Rasha ta zargi Amurka da kitsa korar jami'an diflomasiyyarta 114

Rasha ta zargi Amurka da taka muhimmiyar rawa wajen tunzura kasashen duniya don korar jami’an Diplomasiyyar ta fiye da 140 sakamakon zargin hannunta a yunkurin kisan tsohon jami’in leken asirinta da ke aiki da Birtaniya.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. kremlin.ru
Talla

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce Amurka ce ta yi uwa da makarbiya wajen tunzura kasashen Yammacin Turai daukar matakin ta hanyar batawa Rashan suna ba tare da hakkinta ba.

Korar jami’an Diflomasiyyar Rashan 143 cikin kankanin lokaci da kasashen duniya 24 suka yi, ya zama babban abin tarihin da za a iya cewa bai tafa faruwa ba a tarihi, inda tuni masharhanta kan alakar kasashe ke kallon matakin a matsayin wani salon yaki tsakanin Rashan da kasashen duniya.

Yanzu haka dai kungiyar tsaro ta NATO ta sanar da dakatar da tantance wasu jami’an Rashan 7 duk dai a ci gaba da daukar mataki kan yunkurin kisan Sergei Skripal tsohon jami’in leken asirin Rasha da ya koma aiki da Birtaniya.

Wasu bayanai da sakateren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson ya fitar ya ce matakin gargadi ga Rasha kan katsalandan din da ta ke yi wajen karya ka’idojin kasa da kasa, inda ya ce akwai karin wasu kasashen ma da nan gaba kadan za su katse hulda da Rashan duk dai don hukunta ta kana bin da ta aikata kan Sergei Skripal da yar sa Yulia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.