Fiye da farar hula dubu 200 sun tsere daga Syria cikin wata guda-MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce jumullar fararen hula dubu dari biyu da 35 ne suka tsere daga yankin Idlib a cikin makwanni biyu da suka wuce, yayin da gwamnatin Syria da Rasha suka zafafa luguden wuta da su ke yi akan tungar karshe na ‘yan tawaye.
Wallafawa ranar:
Hukumar kula da aiki jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan mummunar al’amari da ya auko a tsakanin 12 da 25 ga watan Disamba ya kusan mayar da garin Maaret al-Numan kufai .
Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa a yankin ya ce ya ga mutane da dama na barin garin a cikin jerin gwano.
Motocin akori kura ne ke ta zirga-zirga a babbar hanyar da ta hade kudancin yankin Idlib da arewacin Syria, inda suke ta jigilar fararen hula zuwa tudun mun tsira.
Tun a tsakiyar watan Disamba dakarun Syria da ke samun goyon bayan Rasha suka shiga diran mikiya kan mujahidai a yankin Idlib, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi a watan Agusta, da kuma kiraye-kirayen da Turkiya, Faransa da Majalisar Dinkin Duniya ke ta yi na a kwantar da hankula.
Mujahidan kungiyar Hayat Tahrir al- Sham da ke da alaka a da, da kungiyar al - Qaeda ne suka fi rinjaye a yankin Idlib, inda ma shugabansu ya yi kira ga ‘yan kungyar da su yi fito na fito da masu mamaya daga Rasha.
‘Yan gudun hijira akalla miliyan 3 ne ke wannan yankin na Idlib, sakamakon shekaru da aka kwashe ana gwabza fada a wasu sassan Syria. Yakin Syria ya kashe sama da mutane dubu 370, ya kuma daidaita miliyoyi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu