Isa ga babban shafi
HADARIN-HAITI

Gobarar tankin mai ta kashe akalla mutane 60 a Haiti

Akalla mutane 60 ake fargabar mutuwar su sakamakon fashewar wata motar daukar man gas a kasar Haiti, yayin da ake cewar adadin na iya tashi yafi haka.

Yadda ake gudanar da aikin agaji a Haiti
Yadda ake gudanar da aikin agaji a Haiti via REUTERS - REUTERS TV
Talla

Mataimakin Magajin Garin birnin Cap-Haitien Patrick Almonor wanda ya ziyarci inda aka samu hadarin ya bayyana ganin mutane sama da 60 da suka yi mummunar konewa sakamakon hadarin, yayin da Firaminista Ariel Henry yace adadin wadanda suka mutu ya kai 40.

Almonor yace mutanen da ya gani da idon sa sun yi konewar da ba za’a iya tantance su ba saboda illar da wutar tayi musu, inda ya kara da cewar motar da ta haifar da harin ta fadi ne lokacin da take kokarin kaucewa wani babur da ake achaba da shi.

Taswiran Kasar Haiti
Taswiran Kasar Haiti AFP

Rahotanni sun ce faduwar motar ta sa man da take dauke da shi ya kwaranye  akan titi, abinda ya sa mutane mamaye wurin domin dibar sa, kuma abinda ya haifar da gobarar kenan.

Magajin Garin yace akalla gidaje 20 ne suka kone kusa da inda aka samu hadarin, amma kuma babu wani adadi na mutanen da suka jikkata a cikin su.

Wata ma’aikaciyar lafiya a asibitin koyarwar ta Jami’ar Justinien tace basu da isassun ma’aikatan da zasu iya kula da wadanda suka samu raunuka sakamakon hadarin.

Firaministan kasar Ariel Henry ya bayyana zaman makoki na kasa na kwanaki 3 domin juyayin rayukan da aka rasa, yayin da ya umurci asibitin gaggawa domin kula da wadanda hadarin ya ritsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.