Isa ga babban shafi

Jirgin farko dauke da hatsi zai tashi daga Ukraine zuwa Afirka

Jirgin ruwan Brave Commander da Majalisar Dinkin Duniya ke hayarsa zai tashi daga Ukraine zuwa Afirka nan da kwanaki masu zuwa bayan ya kammala lodin alkama fiye da tan 23,000 a tashar ruwan Pivdennyi ta Ukraine.

Wani jirgin ruwa mai dauke da tutar Saliyo mai suna Razoni, dauke da hatsin Ukraine, yayin da hukumomi suka gudanar da wani bincike a tekun Bahar Maliya kusa da Kilyos, a Istanbul na Turkiyya ranar uku ga Agusta, 2022.
Wani jirgin ruwa mai dauke da tutar Saliyo mai suna Razoni, dauke da hatsin Ukraine, yayin da hukumomi suka gudanar da wani bincike a tekun Bahar Maliya kusa da Kilyos, a Istanbul na Turkiyya ranar uku ga Agusta, 2022. REUTERS - UMIT BEKTAS
Talla

Jirgin wanda ya isa tashar jiragen ruwa dake kusa da Odesa, zai taso ne zuwa kasar Habasha, da Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya suka kulla yarjejeniyar a karshen watan Yuli.

Wannan dai shi ne karon farko da kayan agajin abinci na farko da zai isa nahiyar Afirka tun bayan da kasar Rasha ta mamaye Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu a karkashin yarjejeniyar jigilar hatsi ta Bahar maliya

Denise Brown, jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Ukraine, ya shaida wa manema labarai cewa, ana bukatar hatsi cikin gaggawa a Habasha, kuma Majalisar Dinkin Duniya za ta yi kokarin ganin an ci gaba da jigilar kayayyaki zuwa kasashen Afirka da ke fama da yunwa da tsadar abinci.

An ba da tallafin kayan aikin ne da gudummawa daga Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, Hukumar Raya Kasashe ta Amurka da wasu kungiyoyin ba da agaji masu zaman kansu.

MDD ta ce duniya na bukatar abincin Ukraine, kuma wannan shi ne farkon abin da ake fata na agajin gaggawa ga mutanen da ke fama da yunwa a duniya.

Hukumar ba da agaji ta sayi fiye da tan 800,000 na hatsi a Ukraine a bara.

Hukumomin Ukraine ba su bayar da cikakken bayani kan lokacin da jirgin ruwa zai tashi zuwa Habasha ba, saboda dalilai na tsaro.

Yanzu haka dai jiragen ruwa 16 sun tashi daga kasar Ukraine, a cewar mahukuntan kasar, biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma da kasar Rasha, na ba da damar a fitar da hatsi daga tashar ruwan tekun Bahar Maliya ta Ukraine, bayan da aka dakatar da su na tsawon watanni biyar, sakamakon yakin da ke faruwa tsakanin kasashen.

An dai cimma wannan yarjejeniya ne a watan da ya gabata a cikin fargabar cewa asarar kayayyakin hatsin da aka yi a Ukraine zai haifar da matsanancin karancin abinci da ma barkewar yunwa a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.