Yau ake jana'izar Fafaroma Benedict mai murabus
Dubun dubatar jama'a ne suka hallara yau Alhamis domin jana'izar tsohon Fafaroma Benedict na 16 a fadar Vatican, karkashin jagorancin magajinsa Fafaroma Francis.
Wallafawa ranar:
Gawar tsohon babban limamin darikar Katolika na duniya dan kasar Jamus, na ajiye ne a gaban babban cocin St Peter's Basilica, inda daga baya za a binne gawarsa.
A shekarar 2013 marigayin ya zama Fafaroma na farko a cikin shekaru 600 da ya yi murabus daga shugabancin da yake.
Tun kafin wayewar garin yau Alhamis dubun dubatar mutane suka halarci taron nuna girmamawa ga Benedict, wanda ya rasu a ranar Asabar 31 ga watan Disamba, yan da shekaru 95.
Kawo yanzu kimanin mutane dubu 195,000 ne suka suka gabatar da mubaya'ar su ta girmamawa a cikin kwanaki uku da gawar Fafaroma Benedict ta shafe kwance a majami'ar Basilica, in ji fadar Vatican.
Fafaroma Benedict wanda ainahin sunansa shi ne Joseph Ratzinger ya ci gaba da rayuwa a cikin fadar ta Vatican ne duk da matakinsa na murabus a watan Fabarairun shekarar 2013.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu