Isa ga babban shafi

Narendra Modi ya bukaci hadin kai don kawo karshen yakin Ukraine a taron G20

Firaministan India Narendra Modi ya bukaci hadin kan kasashe da kawo karshen rarrabuwar kan da yakin Ukraine ya haddasa wanda ya ce yana kokarin jefa duniya a gagrumar matsala, dai dai lokacin da ake bude taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki da kasar ke karbar bakonci.

Firaminista Narendra Modi na India.
Firaminista Narendra Modi na India. AP - Ajit Solanki
Talla

A jawabinsa wajen bikin bude taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki da ke gudana birnin New Delhi, Modi ya ce idan aka duba matsalolin da aka fuskanta a fannoni da dama kama daga tattalin arziki karancin abinci da kuma hada-hadar kudi baya ga sauyin yanayi da kuma karuwar ayyukan ta’addanci a shekarun baya-bayan nan, hakan manuniya ce ta bukatar da ake da ita wajen hada kai don yakar wadannan kalubale.

Narendra Modi y ace na wannan karo ya zo a dai dai lokacin da ake fama da matsalar rarrabuwar kai tsakanin kasashe, kuma dukkanin kasashe na da tasu matsayar da kuma yadda suke hangen za a iya warware rikicin, haka zalika manyan kasashe ke da alhakin bayar da kariya ga wadanda yakin ya shafa.

India wadda ke jagorancin kungiyar ta G20 a bana, na son shugabancinta ya karkata kan batutuwa masu alaka da yaki da talauci da kuma kawo karshen kalubalen dumamar yanayi, said ai da yiwuwar batutuwa masu alaka da rarrabuwar kai saboda yakin Ukraine su mamaye zaman taron.   

Taron na G20 dai zai sakataren wajen Amurka Antony Blinken da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov wadanda za su hgana da juna karon farko tun bayan haduwarsu ta watan Yuli.

Kasashen yammaci dai na cike da fargabar yiwuwar China ta fara taimakawa Rasha da makamai lura da kasancewarsu kawayen juna dalilin da ya sanya gudanar da wani taron manema labarai a wani bangare na taron G20 don kira ga Beijing game da wannan yunkuri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.