Isa ga babban shafi

Harin kunar bakin wake ya rutsa da gwamnan wani yanki a Afghanistan

Hukumomin Afghanistan sun tabbatar da mutuwar gwamnan yankin Balkh sakamakon kunar bakin wake, mutumin da ya yi kaurin suna wajen yakar mayakan IS masu tayar da kayar baya, rahotanni sun ce lamarin ya rutsa da shi a ofishinsa da safiyar Alhamis din nan.

Mataimakin firaministan Afganistan kan harkokin tattalin arziki Mullah Abdul Ghani Baradar kenan yayin tattaunawa da ministan tsaron Pakistan, Khawaja Muhammad Asif, a Kabul babban birnin kasar, ranar 22 ga watan Fabrairun 2023.
Mataimakin firaministan Afganistan kan harkokin tattalin arziki Mullah Abdul Ghani Baradar kenan yayin tattaunawa da ministan tsaron Pakistan, Khawaja Muhammad Asif, a Kabul babban birnin kasar, ranar 22 ga watan Fabrairun 2023. AP
Talla

Harin da aka kai masa na zuwa ne, kwana guda bayan ya gana da wasu manyan jami’an gwamnatin Taliban da suka kai masa ziyara daga Kabul babban birnin kasar.

Mohammad Dawood Muzammil ya kassance daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin Taliban da harin masu tayar da kayar baya ya rutsa da su tun daga lokacin da ssuka karbi a shekarar 2021 zuwa yanzu.

Ko da yake an samu raguwar rikice-rikice a kasar Afghanistan tun daga lokacin da Taliban din ta karbi mulkin kasar, said ai kuma sha’anin tsaron kasar ya sshiga wani yanayi, sakamakon hare-haren da mayakan IS ke kai wa.

“Mutum biyu ne suka mutu, ciki har da Mohammad Dawood Muzammil, gwamnan yankin Balkh da sanyin safiyar yau” in ji kakakin rundunar ‘yan sandan yankin Asif Waziri da yake shaida wa AFP, tare da cewa harin kunan bakin waken ya auku ne a ofishin gwamnan da ke haw ana biyu a birnin Mazzar-i-Sharif.

 “Harin kunar bakin wake. Bamu da masaniya kan yadda dan kunar bakin waken ya shiga ofishin nasa”, in ji Khairuddin, wani daga cikin mutanen da harin ya rutsa da su, wanda yanzu haka ke karbar kulawa a asibiti.

Hukumomi sun tsaurara tsaro a yankin, said ai sun hana ‘yan jarida daukar hoto, kamar yadda wakilin AFP ya tabbatar.

Da farko dai an nada Muzammil a matsayin gwamnan lardin Nangarhar da ke gabashin kasar, inda ya jagoranci yaki da mayakan IS, kafin daga bisani a mayar da shi zuwa Balkh a bara.

A ranar Laraba, ya gana da mataimakan firaministan kasar biyu da wasu manyan jami'ai da suka ziyarci Balkh don duba wani babban aikin noman rani a arewacin Afghanistan, a cewar sanarwar gwamnati.

Kungiyar IS ta zama kalubale mafi girma na tsaro ga gwamnatin Taliban tun a shekarar da ta gabata, inda ta kai hare-hare kan fararen hula da ma baki da kuma muradun kasashen waje a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.