Isa ga babban shafi

An gano hanyar magamce matsalar yaran da ake haifa ba rai

Masana kimiyya sun gano wasu matakan da idan aka dauka zai rage yawan yaran da ake haifa babu rai a kasashe masu tasowa a duniya.

Malaman jinya na baiwa jarirai kulawa.
Malaman jinya na baiwa jarirai kulawa. Reuters/路透社
Talla

Matakan wadanda masanan suka gano suka ce yana da saukin aiwatarwa, kuma za su taimaka wurin hana haifan yara fiye da dubu 500 da 65 wadanda ake haifa a irin wadannan kasashe.

Masanan sun yi kiyasin cewa kashi daya bisa hudu na jariran da ake haifa a duniya, ana haifensu ne a bakwaine ko a mara kiba, matsalar da suka koka kan yadda aka gagara yin komai akai.

Sun yi kira ga gwamnatoci da kungiyoyi da su kara kaimi wajen kula da mata daga lokacin juna biyu har zuwa haihuwa a kasashe 81 masu tasowa.

Matakan da masu binciken suka gano sun hada da samar wa da masu juna biyun abinci da ke dauke da sinadarai masu kara kuzari da gina jiki, shan kwayoyin aspirin lokaci zuwa lokaci, magance cutar malariya da sanyi tare da ilimantar da masu juna biyu kan illar shan sigari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.